Tambaya:
Jazakhallahu Prof.
But sir idan kanason samu dividend a ina zakayi register? a apps irinsu Bamboo koko a Meristem, APT etc?
Amsata:
Wa iyyakum. A duk wanda ka yi register da shi, primary broker ne kaman su Meristem, APT, dss, ko kuwa 3rd-Party Apps ne kaman Cowrywise, Bamboo, Yochaa, dss, za ka sami Dividend matuqar kamfanin da ka siya Share din su na bayar da Dividend.
Shin ta yaya za ka sani ko kamfani na biyan dividend?
(1) Cowrywise: Mafi sauqin hanyan da na ke dubawa in ga ko kamfani tana biyan Dividend shine ta Cowrywise. Da zaran ka bude shafin kamfanin, za ka ga DIVIDEND YIELD. Idan an rubuta sifili, to ba sa biyan Dividend kenen. Idan kuwa suna biya, to za ka ga adadin da suke biyan din a cikin dari, wato percentage.
(2) Meristem: Wannan broker din na da takarda wanda ta ke turawa duk sati domin bada shawara a kan stocks. A cikin wannan takardan, tana lissafta dukkanin kamfanoni masu biyan Dividend tare da Dividend Yield, da kuma lokacin da ta biya a baya ko kuma za ta biya a nan gaba, tare da Qualification Date, kai har ma da Bonus, wato qarin Shares kyauta da wasu kamfanoni suke bayar wa. Ga Screenshot nan, sannan kuma ga Link din takardan gabadayanta.
Me zai faru idan lokacin biyan Dividend ya wuce amma baka ji Alert ba?
Kafin ka cancanci a biya ka Dividend, dole sai kana da Shares din kamfanin kafin ko kuma har zuwa ranar Qualification Date. Idan ka cancanta, sannan kuma ka ji shiru, to sai ka nemi Registrar din kamfanin, ka tuntube su ta Email domin ka kai koken ka.
Menene Company Registrar?
Registrar, kamfani ne da ke kula da sunan masu hannun jari (Shareholders) na wani kamfani.
Ayyukansa sun haɗa da:
• Riƙe jerin sunayen masu shares
• Tabbatar da adadin Shares da kowa ke da su
• Tura Dividend ga masu Shares
• Gyarawa da sabunta bayanan masu Shares (suna, lambar waya, banki, da sauransu)
• Taimakawa a Rights Issue ko Public Offer
A takaice:
Registrar shi ne “ofishin rikodin” da ke kula da bayanan masu hannun jari na kamfani. Kuma kowace kamfani tana da Registrar din ta. Ga misalan su: Meristem Registrars, First Registrars, Coronation Registrars, CardinalStone Registrars, da dai sauransu.
Ta yaya zan gane Registrar din kamfanin da ni ke da Shares a ciki?
(1) Ta hanyar Internet Search za ka iya neman sunan Registrar din kowacce kamfani tare da Email din su.
(2) Cowrywise: A shafin kowanne kamfani ka bude a Cowrywise, to za ka ga sunan Registrar din kamfanin a can qasa. Idan ka ga sunan, to sai ka nemi Email din su ta Internet Search.
Idan ka tuntube su, za su duba su tabbatar da bayanan ka, sannan daga baya, ka ji Alert.
Wai shin menene Dividend?
Dividend kuɗin riba (Profit) ne da kamfani ke raba wa masu hannun jarinsa (Shareholders) daga ribar da ya samu a zango (Interim Dividend) ko kuma a shekara (Final Dividend).
Misali: Idan kana da hannun jari na kamfani, kuma kamfanin ya samu riba, zai iya ba ka wani kaso na wannan riba a matsayin Dividend. Manya da qananan kamfanoni suna iya biyan Dividend, matuqar sun ci riba.
A da MTN na biyan Dividend, amma kuma da ta fadi a 2024, sai bata biya ba har sai da ta ci riba a 2025 sannan ta dawo da biyan Dividend.
Menene Dividend Yield kuma?
Dividend Yield yana nuna maka nawa kake samu daga Dividend idan aka kwatanta da farashin Share din.
Ana lissafa shi a cikin kashi dari (%).
Misali:
Idan ka sayi share a ₦100, kuma kamfanin ya biya dividend ₦10 a shekara ga kowacce Share,
to dividend yield ɗinka = 10%. Ka ga, idan kana da 1,000 Shares (₦100,000), za ka sami ₦10,000 kenan, idan kuma kana da 10,000 Shares (₦1 Million), za ka sami ₦100,000 kenan.
A takaice:
• Dividend = kuɗin riba da kamfani ke ba masu shares
• Dividend Yield = yawan ribar da ka samu idan aka kwatanta da farashin da ka biya ga kowacce Share.
Idan kana so, zan iya ba ka jerin kamfanonin Najeriya da ke biyan dividend mai kyau.
Kamfanonin da suka fi biyan Dividend
• Banks (UBA, GTB, Zenith, Stanbic IBTC): Interim da Final Dividend
• Dangote Cement da BUA Foods: Final Dividend
• Seplat: Quarterly (sau hudu a shekara)
• Presco, Okomu: Interim da Final Dividend. Sun biya Interim Dividends sau biyu a 2025, ana tsammanin za sub iya Final Dividend bayan sun kammala tattara sakamakon riban 2025.
Ku karanta wannan maqalan, domin qarin bayani.



