Tuesday, October 14, 2025

Lafiyar ‘Ya Mace Jari

Wannan shiri mai suna a sama, sabon shiri ne wanda daya daga cikin mata na Dr. Fatima Mahmud, kwararriyar likitan mata da haihuwa wato Consultant Obstetrician and Gynecologist take gabatarwa duk ranar lahadi tare da Hannatu Aminu Yero, kwararriyar malaman jinya wato Nurse. Dukkanin su su biyun, ma’aikata ne a asibitin koyarwa a ABU wanda ke Shika wato ABUTH.

 

Shirin ya shafi lafiyar ‘ya mace ne, lalurorin mata na yau da kullum tare da lalurorin su wanda ya shafi haihuwa. Mata, ‘yan mata har da iyaye manya za su qaru sosai da bayanan da ake tattaunawa a cikin wannan shirin. Kai har ma maza za su qaru da wasu daga cikin bayanan. Ga lamban wayan da za a iya tura tambayoyi ta WhatsApp: 08143646953 domin a karanta su a cikin shiri mai zuwa.

 

Izuwa yanzu, sun gabatar da shiri guda tara (9) wadanda suke tare da wannan saqon, sannan kuma za ku iya samun wadannan shirye-shiryen tare da wasu shirye-shiryen da suka shafi mata da haihuwa a shafikan sada zumunci mai suna Meet the OBGYN (MTO) a Facebook, Instagram, YouTube, da TikTok a adireshin su ko page kamar haka.

 

Facebook: https://www.facebook.com/drfatimamahmud/

YouTube: https://www.youtube.com/@drfatimamahmud

Instagram: Meet the OBGYN

TikTok: Meet the OBGYN

No comments:

Post a Comment