Tuesday, September 15, 2026

GOOD ENTRY POINTS FOR TRADING & INVESTING

Looking at the All-Share Index (ASI) chart below, it is clear that the Nigerian market has been undergoing a correction since 14 May 2026. Following the strong rally from December 2025 through May 2026, many fundamentally sound stocks have retraced significantly and are now finding new support levels.

For me, this correction is creating interesting entry points for both traders and long-term investors.


Stocks I Find Attractive for Trading

Some of the stocks whose current prices I find particularly interesting for short-term trading include:

TIP — ₦23 – ₦24

NAHCO — ₦129

DANGOTE SUGAR — ₦69

PZ — ₦74

CWG — ₦17

UNILEVER — ₦99

BUACEMENT — ₦269

The figures in brackets represent the entry prices I am watching.

My thinking is to trade some of these positions for potential short-term gains in the region of 10 – 30%, depending on how the market and individual stocks behave. Of course, price targets are not guarantees, and the market can always move differently from expectations.


Stocks to Consider for Longer-Term Holding

Beyond the stocks listed above, there are also several fundamentally sound companies whose prices appear to have stabilised following the earlier rally, with relatively minor fluctuations.

These include Aradel, MTN, HBM (Lafarge), GTCO, Zenith, Jaiz Bank, Seplat, Airtel, UPDCREIT, Dangote Cement, Fidson, NIDF (dividend king), UACN, and others.

Depending on your investment objectives, risk tolerance and research, some of these may also present interesting opportunities for longer-term investors.


Meanwhile, I Am Also Watching the Dangote Refinery IPO

One important consideration is the timing of the Dangote Refinery share allotment. Based on the information provided, the allocation is not expected until around November–December.

It was also mentioned that subscribers with applications of ₦50,000 or ₦100,000 could potentially receive their subscriptions in full. If this happens, larger subscribers may not receive their entire requested allocation, at least initially, until the minimum allocation threshold determined by the company is satisfied.

This is not meant to discourage anyone from investing millions in the IPO. Rather, it is simply a reminder to be realistic about the possibility of receiving less than the number of shares applied for—and therefore not tying up all your available capital in an investment whose final allocation is still uncertain.

There is another interesting dimension.

It was mentioned that approximately 10 million people could subscribe to the IPO, while the company can absorb about 30% oversubscription. With 5.33 billion shares available, dividing that number by 10 million potential subscribers gives approximately 533 shares per subscriber (₦280,000), if everyone were to receive an equal allocation.

And then came the astonishing early demand.

Within just a few hours of the offer going live yesterday, almost ₦1.5 trillion had reportedly been received in subscriptions—even while several fintech platforms, including Bamboo, Cowrywise and Afrinvest, were experiencing difficulties.

If we use the estimated oversubscription threshold of approximately ₦2.795 trillion, the ₦1.5 trillion received within those first few hours already represents roughly 54% of that amount.

Imagine what the subscription figure could look like after the full 30-day offer period.

Please, do not panic if your subscription channel is not working.

As I explained during the live video, IPO allocation is NOT done on a first-come, first-served basis. So, there is no need to rush or worry that you will lose your allocation simply because you could not subscribe immediately.

Relax, take your time, and try again later. You have a 30-day window within which you can subscribe.

Remember: subscription is one thing; allocation is another.

So, stay calm and avoid unnecessary pressure. You will have enough opportunity to complete your subscription within the offer period.


My Personal Approach

For this reason, I am personally considering applying for a relatively small number of shares—perhaps around 1,000+ shares—with the expectation that I could potentially receive a meaningful portion of the allocation.

Rather than committing a very large amount of capital to the IPO and waiting until December, I would prefer to deploy part of my capital into fundamentally sound stocks at attractive entry points, trade some of them for potential short-term gains, and also build longer-term positions where appropriate.

In other words, while I wait for the Dangote Refinery allotment, the market correction itself may be presenting opportunities worth exploring.

As always, do your own research, understand the risks, and invest according to your own financial goals and risk tolerance.


Disclaimer: This is my personal market analysis and strategy, not financial advice or a recommendation to buy or sell any stock. Do your own research before making any investment decision.


Monday, September 14, 2026

Fahimtar Kasuwan Hannun Jari da Dangote IPO

Menene Hannun Jari (Equity)?

Hannun Jari (Equity) yana nufin rabon mallaka da mutum yake da shi a cikin wani kasuwanci ko kamfanin da yake samun riba. Muddin ka sayi hannun jari a kamfani, to ka zama daya daga cikin masu gidan sarautar kasuwancin (masu gida)—ko da kuwa rabo mai matukar kankanta ka ke da shi.

Alal misali. Muhammad and Maryam ne suka bude shagon siyar da wayoyi da jarin ₦100,000, a inda kowannen su ya bada ₦50,000, wato 50 % (Equity) kenan. Idan an sami riban ₦20,000 a shekara, haka za a raba riban ₦10,000 ga kowa. Idan kuma shagon ya bunqasa ya koma ₦1,000,000, ka ga kenan kowa hannun jarin shi, ya koma ₦500,000 kenan (50%). Haka lissafin zai kasance idan ma darajan shagon ya yi qasa.   

Hanyoyi 2 da ake Samun Kudi a Hannun Jari

Rabon Riba (Dividends): Idan kamfani ya yi riba a cikin shekara zuwa karshen, yakan raba wa masu hannun jari wani bangare na ribar. Wasu kamfanin na yin rabon a sau daya ne kawai a karshen shekara (Final Dividend) kaman Dangote Cement, wasu kuma sau biyu – a tsakiyan shekara (Interim Dividend) da qarshen shekara (Final Dividend) kaman MTN, wasu kuma har sau hudu, bayan duk watanni uku (Quarterly Dividend) kaman UPDCREIT.

Karuwar Daraja (Capital Gain): Idan ka sayi hannun jari na kamfani a kan ₦90 kowace tsagi (share) kaman MTN a 2019 sanda ta fara siyar da hannun jarin ta ga mutane, sannan kamfanin ta bunkasa har farashin ya koma ₦800 a yanzu wato 2026, ka samu ribar ₦710 (789%) a kowace tsagi idan ka sayar.

Hanyoyin da za ka iya Zuba Jari a Kasuwan Hannun Jari (Stock Market)

Kasuwan Hannun Jari ta Farko (Primary Market): Wannan ya ƙunshi sanda kamfani za ta fara siyar da hannun jarin ta na farko ga gamagarin mutane domin ta tara kuɗin bunƙasa ayyukan ta wato Initial Public Offering (IPO) kamar yadda kamfanin matatan man fetur na Dangote zai fara siyar da hannun jari ga mutane a 14 ga watan Satumba na 2026.

Kamfani zata iya siyar ma masu hannun jari a cikin ta tsagi mai arha a garesu domin ta bunqasa kamfanin ta hanyar Rights Issue ko Rights Offering (RO), kaman yanda kamfanin sukari na Dagote suka siyar da tsagi a 2026 ga kowane mai riqe da hannun jarinta akan ₦60, bayan a lokacin ana siyar da kowace tsagin hannun jarin kamfanin a kasuwan hannun jari na NGX akan ₦75.

Haka zalika, kamfani zata kuma iya neman qarin kudin gudanarwa ko bunqasa ta ta hanyar siyar ma wadanda ke da hannun jari a kamfanin dama wadanda basu da hannun jari a kamfamin tsagin ta a rahusa ta Public Offering (PO) kaman yanda kamfanin MTN tayi a 2021 a inda siyar da tsaginta akan ₦169.

Sai kuma na qarshen su, wanda kamfani ke siyar da hannun jarin ta a cikin sirri wato Private Placement (PP) ga kebabbun mutane masu kudi sosai ko kuma wata kamfanin a farashi mai rahusa domin su tara kudin yin wasu ayyukan kaman yanda kamfanin matatan man fetur na Dangote ta yi a watan Juni 2026 a inda ta sayar da kowane tsagi akan dala 0.35, a yanzu kuma zai sayar da kowane tsagi a IPO akan dala 0.4 wato ₦525. Kudin da aka samu daga dukkanin wadannan hanyoyi guda 4 wato IPO, RO, PO, da PP suna zuwa lalitan kamfanin ne domin yin wani aiki dashi.

Kasuwan Hannun Jari ta Biyu (Secondary Market): A wannan kasuwan ne kuma mutane suke iya yin hada-hadan hannun jarin da suka siya ta hanyar kasuwan hannun jari ta farko (Primary Market) domin su siyar ga wasu mutanen daban kuma su iya siyan hannun jarin wasu kamfanonin wato Stocks domin amfanuwa da su ta idan sun raba riba (Dividend) ko kuma idan farashin su ya tashi wato Capital Gain. Kudin da aka samu ta wannan hanyan, baya zuwa wajen kamfanin da aka siya ko ka siyar, tana shiga aljihun wanda ya siyar ne kawai wato gamagarin mutane masu riqe da hannun jarin kamfanin ko kuma ma’aikatan kamfanin idan su ne suka siyar da hannun jarin su.

Kasuwannin Hannun Jari Guda Nawa ne?

Akwai kasuwannin hannun jari guda biyu a Najeriya. Wanda tafi shahara kuma babban, it ace Nigerian Exchange (NGX) mai dauke da kamfanoni kaman 144 masu jumillan darajan da ya kai naira tiriliyan 157. Mafi yawancin manyan kamfanonin da muka fi yin hada-hada da su suna NGX ne.

Sai kuma ta biyu, wanda qarama ce ana kiran ta da NASD OTC wanda ke dauke da kamfanoni 46 masu darajan da ya kai naira tiriliyan 2.7.

Yanda za ka iya Siyan Hannun Jari

Dillalan Hannun Jari (Stock Brokers): Zaka zabi daya cikin dillalan hannun jari daga cikin sama da 500 domin bude akawunt da su amma fa ka tabbatar wanda ka zaba, yana da rijista da SEC (Securities and Exchange Commission). Sanannu daga cikin wadannan dillalan sun hada da Afrinvest, InvestNaija, Cowrywise, Bamboo, CardinalStone, APT, Trove, Atlass, United Capital, Meristem, da dai sauransu. Yawancinsu zaka iya sauke manhajar su a waya, kadan daga cikin su kuma dole sai dai kayi amfani da komfuta wajen amfani dasu yanda ya kamata kaman Atlass da United Capital.

Bude Akawunt: Kafin ka iya siyan hannun jari, ana da buqatan da ka bude akawunt wato Brokerage Account ko kuma abinda yanzu akafi sani da CSCS Account a wajen dillalan hannun jari wato Stock Brokers. Irin wannan akawunt din ana bude shine kaman yanda zaka bude akawunt din banki a inda zaka cike bayananka tare da adireshin ka, da bayanan bankin ka irin su BVN, sannan kuma ka tura musu da shaidan adireshin ka wanda yake dauke a kudin wuta ko ruwa da bai wuce watanni uku a baya ba. Dole akawunt din bankin da zaka bayar ya kasance banki ne wanda yake Deposit Money Banks kaman irin su GTB, Zenith, UBA, banda irin su OPay ko Moniepoint. Idan ka kammala dukkanin wadannan, za ka jira kwanakin aiki 2 zuwa 7 kafin a fitar maka da lambobin akawunt dinka guda biyu, wato CHN (Clearing House Number) da CSCS (Central Securities Clearing System). Shi dai CHN kaman BVN din ka ne na banki, baya canzawa, koda kuwa ka qara bude wani CSCS akawunt din da wani dillalin daban. Shi kuwa CSCS kaman lamban akawunt dinka ne na banki, wanda zai iya canzawa idan ka bude wani akawunt din a wani bankin daban. Da zaran an kammala buda maka akawunt dinka, sai ka sa kudi, daga nan kuma ka zabi duk kamfanin da kake son siya a NGX domin ka siya a lokacin hada-hadan hannun jari wato, kwanakin aiki, daga 9.30 am zuwa 3.50 pm. Akwai kamasho wato commission da ake biya idan ka siya ko ka siyar da hannun jarin ka. Kudin kamashon ya danganta ne da dillalin da kake amfani da shi. Amma mafi yawanci, suna cire 1.8% ne idan zaka siya, sannan kuma su cire 2.2% idan zaka siyar, jumla ya kama 4% kenan. A sani na, Atlass ne wanda ya fisu sauqi a inda yake cire make 0.8% idan za ka siyar, jumla yak ama 2.2% kenan, sannan kuma ya cire make 1.37% idan zaka siyar. Sai kuma United Capital wanda yake cajin kusan 3.2% gabadaya siye da siyarwa. Zaka iya siyan tsagi daya kacal, ko kuma da yawa wato iya kudin ka iya shagalinka. Amma idan dillalin da ka zaba shima yana aiki ne da wani dillalin kaman Cowrywise, Bamboo, ko Yochaa, to dole tsagin da zaka iya siya na kowane kamfani ya kasance ya kai qiman ₦5,000. A irin su Afrinvest, Meristem, Atlass, ko APT kuwa, zaka iya siyan tsagi daya kaman na Jaiz Bank wanda ake siyarwa a kan ₦8. Saboda haka, da talaka da mai kudi dukkanin su za su iya cin riban hada-hada a hannun jari. Idan kana son siyan hannun jarin NASD OTC, shima sai ka bude akawunt da dillalin ka, idan yana hada-hadan NASD OTC kafin kafa siya da siyarwa a kasuwan. Shi NASD OTC yanada manhaja ne guda daya a inda akeyin hada-hadan kamfanonin shi.

Babban Darasi Kafin Ka Fara Siye Da Siyarwa

Ilimi (Knowledge): Ka tabbatar ka nemi ilimin kasuwan hannun jari kafin ka fara hada-hada a kasuwan domin gudin yin asaran kudin ka saboda akwai sarqaqiya a kasuwan sosai. Ilimi ne kadai zai sa ka iya cin riban da ya kamata ba tare da asara ba. Akwai masu karantarwa da yawa a YouTube (Nairametrics, Wealthcoachomiete, Salihu Lukman) da dai sauran su. Ya zama dole ka laqanci yanda ake siya ko siyar da tsagi (share) ta Limit Order ko Market Order. Idan ka laqance su, zaka fahimci cewa Limit Order ne ya fi dacewa ka dunga amfani da shi a kodayaushe domin yafi samar da rahusa wajen siya da kuma riba wajen siyarwa. Dole ka fahimci yanda zaka harhada kamfanoni domin su tabbatar da cewa samun riban ka ta yanda ko da daya daga ciki yayi qasa, to wani zai tada shi domin ka sami riba a koda yaushe wato Diversification.

Manufa (Objectives: Dole ka qudurce manufan ka a yayin hada-hadan hannun jari. Shin kana so idan ka siya ka riqe ne na lokaci mai tsawo kama shekara 3 ko 5, wato Long-term Investor ko kuwa kana jujjuya hannuwan jarin ka ne domin samun riba ta yanda za ka siya idan sun sauka, sannan ka riqe na zuwa lokacin da za su farashin su zai tashi sai ka siyar ka nemi wani mai sauqin farashi ka qara siya wato Trader. Zabin manufanka tun ran gini ran zane zai taimake ka wajen zaban ire-iren hannuwan jarin da za ka siya. Shin Trader ka zaba ko kuwa Long-term Investor, dole kuma ka laqanci yanda zaka sami hannun jari a rahusa idan za ka siya wato Entry Price. Alal misali, kasuwan ya fara tashi daga Disamba 2025 har zuwa Maris a sa’ilin da ya dan fara hutawa har zuwa Afrilu, daga nan kuma ya qara yin wani goron zabin tashin har tsakiyar Mayu a dalilin sanarwan da FTSE Russell sukayi na daga martaban kasuwan hannun jarin Najeriya tare da qara ma masu jujjuya kudaden ‘yan fansho daman siyan hannayen jari fiye da yanda hukuma ta qayyade musu. Tun daga nan y afara sauka kadan-kadan, har izuwa qarshen Juli, ya cigaba da sauka a Agusta har zuwa 27, wato ranar da FTSE Russell ta tabbatar da cewan zata daga martaban NGX a 21 ga watan Satumba 2026 bayan dakatar da wannan qudirin da tayi a watan Juni. Dole ka laqanci ire-iren wadannan hawa da saukan da hannayen jari keyi sannan ka laqanci daidai lokacin da yakamata ka siya mai rahusa ko kuma ka siyar domin ka sami riba mai kyau.

Halayyan Cinikayya (Investment Personality): Ya kamata ka fahimci irin halayyan cinikayyan ka. Shin zaka iya siyan hannun jarin da yake sama da ƙasa ko da kuwa mai qarfi ne kaman MTN, ko Dangote Cement, ko kuma yake iya tsayuwa ba tare da ya daga ba na tsawon lakaci kaman Airtel (sai da ya tsaya na kusan shekaru 2 a wuri daya), ko kuma wanda yake tsayuwa na wani lokaci kafin ya dan daga kadan kaman Seplat?

Bangarori 5 Masu Kawo Riba

Halal: Wannan bangaren yana qunshe da manya-manyan kamfanoni ne har guda 12 wadanda aka tantance ayyukan su kuma a tabbatar da cewa suna bin abin da Shari’an musulunci ya gindaya wajen harkokin su wato Shari’ah-Compliant. Ga wasu daga cikin su tare riban da suka kawo a cikin wannan shekaran kawai wato Year-To-Date (YTD) Sun hada MTN (59%), Dangote Cement (70%), HBM Lafarge a da (153%), Jaiz Bank, Aradel (111%), NASCON (49%), PRESCO (41%), BUA CEMENT (56%), da dai sauran su. Amma fa ka sani cewa riban da aka samu a baya ba ya nuna cewa haka za ayi ta samu a nan gaba ma saboda kasuwan taba caccanzawa. Ka sani cewa ba wai guda 12 dinnan ne kawai suke Halal ba. Bincike ya nuna sun kai 53 daga cikin 144 wadanda aka tantance su da cewa Halal ne.

Mai Da Gas: Wannan bangare na dauke da kamfanoni guda 7, mafi kawo riba daga cikin su sune Seplat (157%) da Aradel (111%). Ina son Seplat sosai saboda yanda yake tsayawa cik na dan wani lokaci sai kuma ya tashi. Hawa da saukan kasuwan bai cika shafan shiba. Na fara siyan Seplat shekaru biyu da suka wuce a 2024 akan ₦3,300 kowane tsagi daya, a yau ana siyar da kowani tsagi akan ₦16,000 wato ya kawo riban 385% kenan ga wanda ya siya ya riqe har shekaru biyu kacal. 100,000 ta koma ₦485,000, haka nan ₦1,000,000 to koma ₦4,850,000, bayan riban da ka kwasa wato Dividend, ba tare da ka yi komai ba. Wannan ya ninka kusan sau 5 kenan a cikin shekaru 2 kawai, shin idan ace gida ne ko fili ka siya, za su iya ninkawa haka a cikin wannan dan qanqanin lokacin?

Banki: Bankunan da suka fi qarfi daga cikin bankuna 14 sune Zenith (103%) da GTCO wato GT Bank (43%). Sauran sun hada da First Bank (184%), Ecobank (77%), Jaiz Bank (69%) da kuma Stanbin IBTC (54%).

Kayayyakin Amfani: Akwai kamfanoni da yawa a wannan bangaren, sun kai 15 – 19. Wadanda suka fi kawo riba a wannan shekeran kuma masu qarfi ne sun hada da PZ (87%), NASCON (49%), Unilever (53%), Vitafoam (111%), Nestle (43%), da UNIONDICON (244%) amma na qarshen bata da qarfi kaman sauran, a kula da kyau.

Sadarwa (ICT): Akwai kamfanoni guda 9, amma manya a cikin su sune Airtel (178%)  da MTN (59%). Daya daga cikin marasa qarfi a cikin su shine NCR (122%).

Me Ya Sa Aka Bar ‘Yan Arewa A Baya A Kasuwar Hannun Jari?

A ganina, abubuwa 2 ne suka sa a ka bar ‘yan Arewa a baya a fannin hannun jari. Na farko dai idan za ka yi la’akari da sauran fannonin rayuwa na karatun zamani kaman irin su lauya (Law), likitanci (Medicine) and jinya (Nursing), injiniya (Engineering) da ilimin tattali da banki (Banking and Finance) zaka ga cewa ‘yan Kudu sun yi ma ‘yan Arewa nisa sosai a baya kaman shekaru 30 – 40. Amma a hankali, sai ‘yan Arewa suka fara yin boko ka’in da na’in, har suka kai ga zama manyan malamai na jami’o’i a Arewa wanda ada mafi yawanci ‘yan kudu ne. A yanzu ‘yan Arewa suna karantan dukkanin fannonin ilimin boko sosai wanda ya hada darussa kaman su Economic, Accounting, Banking and Finance, da dai sauran su.

Dalili na biyu kuma shine addini. Za ka samu wadan su malaman a baya suna yin nuni da cewa musulmai su guji gabadaya kasuwan jari (Capital Market) ko na hannun jari (Stock Market) domin a ganin su haramun ne saboda suna amfani da kudin ruwa (Interest). Haka ya sa mutanen mu da yawa suka guje ma duk wani darasi na Accounting, Banking, ko Economics tare da guje ma duk wani aiki a banki ko inda ya shafi jari (Investment). A hankali, sai aka fara fahimtar cewa ashe za ka iya yin kasuwancin ka a cikin kasuwan hannun jari bare da yin mu’amala ruwa ba. Wannan shiyasa na fara daukan bangaren da yake na Halal ne a sama domin yin qarin bayani. A hankali kuma, wasu na ganin yanda wadanda suka sa hannun jari suke diban garabasa a cikin sauki ta hanyan siya da riqewa kawai na tsawon lokaci ba tare da shan wani wahala ba. A hankali a hankali sai mutanen mu suka qara qaimi wajen fahimtar kasuwan da kuma qin bin hanyoyin macuta wato Ponzi Schemes a inda za a ce wai za a dunga ribanya maka kudinka duk sati ko duk wata.

Shin Ya Kamata Ka Siya Hannun Jarin Kanfanin Mai Na Dagote?

Kamfanin man fetur na Dangote zai fara siyar da hannun jari ga gamagarin mutane kaman ni da kai a ranar litinin, 14 ga watan Satumba, har izuwa 13 ga watan Nuwanba, wato har tsawon wata guda cir ta hanyar IPO. Ya fara siyar ma manyan kanfanoni da masu kudi ta hanyar Private Placement a cikin wat Yuni a inda ya tare $2.5 Biliyan. A yanzu kuma, yana son tara $1.6 biliyan ne ta hanyar siyar da tsagi 4.1 biliyan ga mutane. Wannan kamfanin, zata kasance mafi girma a Africa, sannan kuma tana kan hanyan zama matatan man da tafi kowane girma a duniya a nan ‘yan shekaru kadan. Wannan wata dama ce ga kowa da kowa domin ya sami siyan wannan hannun jarin, saboda dai wannan kamfani tana da riba sosai, kuma bisa ga dukkanin alamu, masu jari a kamfanin za su ribauta a nan gaba. Kada ka bari a bar ka a baya. Yi maza-maza ka bude akawunt kaman yanda na yi bayani sama, sannan ka tanadi ‘yan kudin ka domin siyan wannan hannun jarin. Mafi qaranci shine ₦5,250 wato tsaguna 10, daga nan kuma, zaka iya qarawa goma-goma har izuwa kudin ka.

Shin Zan Iya Sayen Dangote IPO Idan Bani Da Akawunt Din Dillalai (CSCS Account)?

Eh, za ka iya siya wannan IPO din ko da kuwa ba ka CSCS Account a yanzu. Daga baya idan bude akawunt din, sai ka tuntubi masu riqe da hannun jarin kamfanin gabadaya wato Coronation Registrars, ka basu lambobin CSCS Account din ka, domin su saka maka shares dinka.

Sauran bayanin da ke qasa, na tattake wuri wajen yin sharhi mai tsawo a game da su a bidiyon da nayi a Zoom. Za a iya sauraron cikakken bayanai ta YouTube:

 https://www.youtube.com/watch?v=rW1qTFPCyY8&lc=UgwoE6GhfBXRoJYn1vN4AaABAg

Hadari (Risk)

Hawa da Saukan Farashi (Price Movements)

a.    IPO (Aradel, Seplat, MTN, etc.)

b.    Sauran hannun jari (ASI)

c.    Fixed income market (Sukuk, bonds, CP, etc.)

Jari (Capital)

a.    Ajiya (Savings)

b.    Kudin haya (Rent)

c.    Kudin makarantan yara (School fees)

d.    Bashi (Loan): Private, Bank, Loan apps

e.    Yanda zaka iya siyan tsaguna (shares) da yawa.