Wallahi fate duniya ne! Ga dadi, ga qara lafiya tun ma ba idan ace ta ji kayan hadi irin su alayyaho, albasa mai alwashi, attarugu, tattasai, oats, da dai sauran su, sai kaga maigida yana ta share hanci yana cewa a qaro a qaro har sai ya tada tukunyan gabadayan shi. Ba fa santi nake yi ba, mu da ma Zage-Zagi ai an san mu da shan fate kaman yanda aka san Kanawa da gurasa. Shin kai Bazazzagin asali ne ko kuwa dan Cotonou, idan dai har dan asali ne, to ka tabbata cewa kana tayar da daro guda na fate a qalla duk sati idan kuma ba haka ba to za a bincika Indigene din ka a tantance
Amma fa idan faten tsaki za’ayi, to kada a surfe masaran domin wannan dussan da ake cirewa, yana dauke da sinadaran gina jiki masu dimbin yawa. Kusan babu sinadarin qara lafiya da gina jiki kaman su Vitamins da Minerals da babu a fate. Ko wani irin fate kuwa, zaka iya cancanzawa a tsakanin faten tsaki, oats, wake, acca, alkama, da dai sauran su.
Da taimakon Allah ta hanyar fate na karya laggon Diabetes a 2016 a inda na daina cin duk wani abinci sai dai fate kadai har sai da sukarin jinina ya sauko, ya kuma daidaita a cikin ‘yan kwanaki kadan, na kuma daina shan maganin Diabetes. har ila yau kuma sukarin jinina yananan lafiya lau.
Kada ka sake ka auri wanda bata iya fate ba, uwargidan da bata iya ba kuma, tayi marmaza taje ta koyo. Shin ko kin iya fate?
No comments:
Post a Comment