Sunday, April 27, 2025

Me Yasa Bahaushe Ke Musanya Haruffan F da P Wajen Furuci?

Dr. Salihu Lukman 

Gabatarwa

Akwai Hausawa da dama, da ma wadanda ba asalin Hausawa ba ne mazauna Arewa musamman Musulmai da suke musanya duk harafin F da P sannan kuma su musanya duk harafin P da F wajen magana, wato yayin furta su a cikin kalmomi. Mutane da yawa suna mamakin me yasa hakan ke faruwa, tun ma ba wadanda ba Hausawa ba. Kuma wadanda ke musanya wadannan haruffan ba sun taqaita da marasa karatun boko ne mai zurfi  ba kawai, a’a, har wasu masu zurfin karatun boko kaman masu diploma ko digiri na daya ko na biyu har ma masu digir-digir zasu iya yin wannan kuskuren. Kadan daga cikin wasu manyan mutanen da suke yin irin wannan kuskuren a wani lokaci sun hada da tsohon shugaban qasa Muhammadu Buhari da ministan shi na shari’a kuma Attorney General wato Abubakar Malami, SAN. Ga wanda yake kallon fina-finan Hausa kuwa, za ka ga cewa mafi yawancin ‘yan wasan Hausa da kuma mawaqan Hausa suma suna yin wannan kuskuren akodayaushe. Misali anan sun hada da Presido na Labarina da kuma Alan Waqa a cikin waqoqin shi. Akwai abokaina da yawa da nasan suna yin wannan kuskuren duk da cewa sun yi digiri kuma haziqai ne sosai wasu ma kila sun kai matakin qarshe na koyarwa a jami’a wato professor. A matsayina na Bahaushe – duk da yake asalina ni Fulani ne gaba da baya na – wannan kuskuren ya dade yana bani mamakin shin me yasa hakan ke faruwa ga Hausawa da kuma wasu qabilun wadanda suke zaune a Arewa sannan kuma suka kasance Hausawane a al’adance kaman ni. A sabili da haka ne na ke son fitar da bayanin abin da yasa wannan kuskuren ke faruwa a dan binciken da nayi gami da fahimta na.

Qarin Bayani 

(1) A cikin haruffan Hausa babu P kwata-kwata: Wannan ya faru ne saboda asalin rubutaccen Hausa an fara shine da harruffan Larabci wato Ajami, shi kuma Larabci ba shi da harafin P kwata-kwata. Saboda haka Bahaushe ba zai rubuta maka harafin P ba a kalman da take asalin ta daga Hausa ne. Misali anan shine kalman Fate ko haraFi, ba zai taba rubuta maka su da P ba wato Pate ko haraPi sai dai Fate ko haraFi. Shi kuma Balarabe, a duk inda zai karanta kalma mai qunshe da P, to zai canza harafin P ne zuwa B. Misali: Panda (sunan wata shahararriyar kasuwa ce a Saudiyya), sai ka ji Balarabe ya ce Banda. 

(2) Bahaushe  ba ya furta harafin F a cikin zance idan kalman asalin ta daga Hausa ne: Kalli wadannan kalmomin: fanfo, fada, fatanya, farfagiya, fafutuka, janfa, da sauran su. Dukkanin su Bahaushe zai musanya F din da ke cikin kalmomin ne da P idan yazo furta su duk da yake zai rubuta su ne da harafin F ba P ba. Wannan ya shafi har sunayen da asalin su daga Larabci ne kaman Halifa, Fati ko Fatima, Farida, Fa’iza, da dai sauran su. Shin tun Hausawan farko ne suka samar da qin furta harafin F idan ya zo cikin kalmomin Hausa tun kafin zuwan Musulunci ya kawo harafin F sannan kuma ‘yan baya suka kwaikwaye su har ya iso mana? ‘Yan zamanin yanzu, na kan ji wasu Hausawa wadanda boko ya shige su da kyau ko kuma tashin birni wato kaman ince ‘yan gayu kenan, suna furta F a kalmomin Hausa kaman kalmomin da na yi misali da su a sama. Wannan sabon abu ne a Hausa. Mai karatu zai yi tambayan cewa to wai shi mallam Bahaushe ba ya iya furta harafin F ne kwata-kwata da yake rubuta ta ta amma kuma sai ya musanya ta da P idan ya zo furuci?

(3) Bahaushe ya iya furta harafin F a zance: Saboda yanda rubutun Ajami ya samo asali daga haruffan Larabci wadanda suke dauke da harafin F, Hausa ma na dauke da harafin F, sannan kuma Bahaushe ya iya furta harafin F saboda iya karatun Alqur’ani mai girma da yayi. A ganina, Bahaushe baya furta harafin F kafin zuwan Musulunci. Saboda haka, da Musulunci ko Larabci ya kawo mai harafin F, sai ya koye shi amma kuma sai ya cigaba da furta P a duk zancen shi na Hausa sai dai idan zai yi karatun Alqur’ani ne, to sai ya furta F. Wannan yasa ko da Bahaushe ya iya rubutun Hausa da haruffan turanci, to sai ya rubuta kalmomin Hausa da F saboda baya rubuta P a Ajami amma kuma sai ya furta ta da P saboda haka ya saba fadan kalmomin Hausan tuntuni.

(4) Me ya faru kuma da kalmomin turanci? Idan ka fahimci bayanaina daga (1) zuwa (3) sosai, zaka ga cewa Bahaushe zai rubuta kalman Hausa mai dauke da F kaman Fara amma kuma sai ya musanya F din da P wato Para idan zai yi furuci. Wannan shiyasa wasu daga cikin Hausawan ko kuma wadanda suke Hausawane a al’adance suke musanya harafin F da P a duk wata kalman turanci kaman yanda suka saba yi ga kalmomin Hausa ba tare da sun sani ba. Misali sun hada da Fans, sai ka ji sunce Pans, Facebook, sai ya kaji sunce Pacebook, Film sai ya koma Pim, Facetime sai ya koma Pacetime, da dai sauransu. Irin wannan musanya F da P a wajen furuci, sai ya wanzu ga kalmomin da suke dauke da harafin P a inda zaka ji shi kuma sun furta shi da F ba tare sun yi la’akari da hakan ba. Misali sun hada da Prince, sai ka ji sunce Frince, Pen sai ya koma Fen, Poverty sai ka ji sunce Foverty, da dai sauransu. A ganina irin wadannan canje-canjen da sukeyin ma kalmomin wajen furucin su, ba su ma san cewa suna yi ba kwata-kwata kuma ba haka yake nuna cewa su jahilai ne ko daqiqai ba. Wasu daga cikin Yarbawa ma tun ba wadanda suka taso a kudu ba, su kuma sai kaji suna share harafin H a duk inda take a kalmomin turanci. Misali, Head sai ya ka ji sunce Ead, Hand sai ya koma And, da dai sauransu. Wani lokaci, har a rubutu, za ka ga cewa suna shafe harafin H a kalmomin turanci. Yarurruka na duniya da dama sunada ire-iren wadannan sauye-sauye saboda yanda yaren su yake kaman yanda nayi cikakken bayani yanda Hausa yake.

No comments:

Post a Comment